Revelation of John 15

1Sai na ga wata alama cikin sama, babba mai ban mamaki: Akwai mala’iku bakwai rike da annobai bakwai, wadanda sune annobai na karshe domin da su ne fushin Allah zai cika.

2Na ga wani abin da da ya bayyana mai kama da tekun gilashi mai haske garwaye da wuta. Tsaye a gefen tekun sune wadanda suka ci nasara a kan dabban da siffarsa, da kuma lambar da ke wakiltar sunansa. Suna rike da molayen da Allah ya ba su.

3Suna rera wakar Musa, bawan Allah, da wakar Dan Rago: ‘’Ayyukan ka manya ne da ban mamaki, Ubangiji Allah, Mai iko duka. Adalci da gaskiya hanyoyinka ne, Sarkin al’ummai. 4Wanene ba zai ji tsoron ka ba, Ubangiji, ya kuma daukaka sunanka? Domin kai kadai ne mai tsarki. Dukan al’ummai za su zo su yi sujada a gabanka domin an bayyana ayyukan ka na adalci.”

5Bayan wadannan abubuwa na duba, kuma aka bude haikalin alfarwar shaida a cikin sama. 6Daga wuri mafi tsarki mala’iku bakwai masu rike da annobai bakwai suka zo. Suna sanye da tufafi masu tsabta, da lallausar linin mai haske, suna kuma da damarar zinariya a kirjinsu.

7Daya daga cikin rayyayun halitu hudu ya ba mala’iku bakwai tasoshin zinariya bakwai cike da fushin Allah wanda yake raye har abada abadin. Haikalin ya cika da hayaki daga daukakar Allah da kuma ikonsa. Ba wanda ya iya shigarsa har sai da annoban nan bakwai na mala’ikun nan bakwai suka cika.

8

Copyright information for HauULB